Ilimi gishirin zaman duniya. Idan babu ilimi, babu rayuwa mai kyau. Kamar yadda aka sani a Musulunci, ilimi wajibi ne ga namiji ko mace. Mace kamar namiji, akwai bukatar ta yi ilimi domin ita uwa ce, ita ke renon ’ya’ya, kuma halaye da dabi’unta abubuwan kwaikwayo ne ga ’ya’yanta.

A lokutan baya, ba a ba mata damar neman ilimi sosai ba, hasali ma, ilimi ba a damu a ba su ilimin addini ballantana na zamani. Har ana cewa “Sabbi saukar Mata”. Watau da sun kai Suratul Sabbi shi ke nan sun bar karatu da neman ilimi.

Mace a wancan zamanin, idan ta kai shekara 14 ko 15 sai a yi mata aure. Hakan yana da kyau kamar yadda addinin ya nuna. Yin aure bai kamata ya hana ilimin mata ba. Abin takaicin sai a bar su a gida ba su san yadda ake tsarki ba.

Hakika ilimin ‘ya mace na da muhimmanci kwarai. Don haka ne ake cewa idan ka ilmantar da ‘ya mace to ka ilmantar da al’umma. A wannan takaitaccen makala zan dan tattauna ne a kan muhimmancin karatun diya mace, kuma karatu mai zurfi na Boko da na Islamiyya.

Yana da matukar muhimmanci mata mu yi karatu. Ya zama wajibi kuma farilla ne a kanmu mu, dalilin kuwa Hadisin nan na Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi wanda ya ke cewa ‘Dalabul ilmu faridatun ala kulli muslimin wa muslimatin,’ wato neman ilimi farilla ne ga dukkan musulmi na miji ne ko mace.

A bangaren karatun Likitanci da kuma Unguwarzoma, wadannan sashi ne da mata za su fi mayar da hankali, domin hakan zai amfani al’umma. A wasu Asibitocin, maza ne wadanda ba muharramai ba ke duba mata. To a maimakon haka, zai fi kyau a ce mace ta duba ’yar uwarta

Mafi yawancin tsokacin mutane a kan karatun ’ya’ya mata a kan yanayin makarantun ne. Yadda ake hada maza da mata, yadda tsarin sanya tufafi yake da sauransu. Idan har gwamnati na so ta habaka ilimin mata a Nijeriya, musamman a Arewa, ya zama dole ta yi la’akari da halayya da addini da zamantakewa da kuma al’adun mutune wajen tsara makarantu da kuma yadda ake karatun, haka zai taimaka sosai wajen bunkasa ilimi sosai a Arewacin Nijeriya.

Ina so mata su sani neman ilimi wajibi ne, sai dai su sani ya zama dole su tsare kansu daga aikata dukkan ayyuka marasa kyawu, iyaye su sanya idanu wajen lura da yadda ’ya’yansu mata suke karatu.

Muhimmancin ilimin ‘ya mace.

1. Mace mai ilimi itace za ta san yadda zata tafiyar da gidanta da kyau idan tana da hankali.

2. Mace itace uwa, ita za ta sa yaranta a kan hanya, har shi mijinta da kan sa ita kan koya masa dabi’u masu kyau. In kuwa ba ta da ilimi, ba ta san abin da ya kamata ta na iya zama masa da ‘ya’yansu, ya zama makauniyar jagora.

3. Turawa ma sun ce duk namijin da ka ga ya yi nasara a rayuwarsa, to akwai mace bayansa – ko uwarsa ko matarsa.

Ilimi ke sanya mace ta san yadda za ta tafiyar da kanta a kowane irin hali. Za ta zama wayayyiya mai basira.

Me Ke Zama Cikas Ga Ilmin ‘Ya’ya Mata?

Ilimin ‘ya mace yana da matukar muhimmanci ga ita kanta da al’umma ba ki daya, wanda a saboda haka masu iya magana suke cewa, idan an ilmantar da ‘ya mace guda daya tamkar an ilmantar da al’umma ne ba ki daya. Sai dai wani hanzari ba gudu har yanzu ana samun wasu dalilai da suke zama cikas ga ilimin ‘ya’ya mata wadanda suka hada da:

Talauci: Talauci na matukar zama cikas a harkar ilimi ga ‘ya’ya mata. Wannan kuwa ya zama ruwan dare gama duniya.

Al’adu: Wasu daga cikin al’adu da ake da su musamman a Arewacin Nijeriya suna zama cikas ga ilmantar da yara mata alal misali har yanzu akwai iyayen suke ganin amfanin mace bai wuce ta yi zaman aure a gida.

Saurin Aure: Yi wa mace aure da wuri yana sanya ta sami cikas a bangaren neman iliminta, amma a nan akwai wadanda suke da aurensu ne amma suka yi karatu na zamani da na addini sai dai ba su da yawa.

Rashin Sani Ga Iyaye: Wannan ma ya kan kawo wa ‘yan mata cikas a wajen neman iliminsu domin kuwa ba za su sami wani goyon baya ba daga wurin iyayensu kasancewa iyayen nasu ba su san muhimmancin ilimin ba ballantana su sanya yaransu su yi.

Saboda haka yanzu kowani namiji ya gane bai son auren jahila. Kowa yana son ya ga yaransa sun zama masa abin alfakhari. Haka kuma zai samu ne idan mace na da ilimi.

Kuma karatu baya tsufa, ko kuwa mutum baya tsufa ya ce ya wuce lokacin karatu. Karatu na farawa ne daga haihuwa har zuwa mutuwa.
Saboda haka ina kira ga ‘yan’uwana mata da kada mu yi kasa a gwiwa mu dage kuma mu hada da addu’a da neman zabin Allah, Allah ya taikama mana ya bamu sa’a a kan komai idan ya kasance na alkairi ne Amin.

conned from Leadership Hausa