Kafun zuwan wayewar kai da ilimi, mata basu da fada aji a al’umma. An dauki mata ba abakin komi ba face masu dawainiyan gida da kula da ‘yara. A zamanin jahiliyyah a kasar Saudiya birne ‘ya’ya mata akeyi da ransu, mata basu da gado, an dauke su kamar rigar da ake canzawa ko wani daqiqa aka ga dama. Karatun ‘ya mace ba karamar amfani yake da a al’umma ba. Sabili da mahaifiya ita ke tare da yara kullum a gida, ilimin zai sa kanta ya waye ta san muhimmancin karatu, zuwa asibiti, bawa yaranta tarbiyyah na kwarai ta inda har zasu zama masu kishin kasa. Mace mey ilimi zata taimaka gurin bawa mijinta shawarwari masu amfani da zasu taimaka wurin gudanar da harkokin yau da kullum. Har ila yau, yara mata dake karkara ana tauye musu hakkin su na rashin samun ingantaccen ilimi ta hanyar aurar dasu tun a shekarun da basu wuce kirgen dangi ba. Wala Allah in tasami miji mey kishin karatu yasakata, wala Allah kuma ta qare da jinyar yoyon fitsari bayan mijin yamata sakin wulakanci. Ba addinin da ya hana neman ilimi a duniya. Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace neman ilimi wajibi ne akan kowani musulmi , Tirmidhi ne ya ruwaito shi lamba ta saba’in da hudu. Rashin wayewar kai ke kai yara da dama zuwa ga halaka. In abu ya shige musu duhu basu isa su tunkari iyayensu ba, sabida al’adan malam bahaushe ya hana yin hakan. karshe shawaran abokanaye da qawayensu zasu dauka wanda ba lallai ne yazama na kwarai ba. Shawarar da zan bawa gwamnati shine, a saka dokan dole sai yarinya ta kai shekaru sha shida kafun a aurar da ita. Aqalla kafunnan ta kara sanin ciwon kanta, ta gama karamar mataki na makarantar gaba da firamari da kuma ilimin yin ginshiqan musulunci batare da ta kwafsa ba. A kuma saka taran duk mahaifi koh marikin yarinyar da ya aurar da ita kafun shekarun da aka qayyade koh ya hana ta zuwa makaranta ya biya naira dubu dari biyar koh zaman gidan maza na shekaru biyar.