Bayan wadannan sana’o’i, wadanda mafiyawancinsu maza ne suke aiwatar da su, akwai wadanda mata ne kawai suke yin su, kamar kadi wanda ake yi don samar da zare da abawa ga masu yin sana’ar saka. Haka kuma matane suke yin sana’ar kitso ga ‘yan uwansu mata. Suna yin salon kitso iri-iri don yin kwalliya ga kan mata wanda yake kara musu kyau da jawo hankalin maza. Akwai kuma sana’ar dakau wadda mata suke karbo hatsi don yin dakau na fura ko garin da za a yi amfani da shi don yin abinci. Wadannan sana’o’i na mata suna taimaka masu yin hidimominsu na yau da kullum da kuma yin bikin dangi ba tare da sun dogara kan wani ba.

Matsayin Sana’o’in Gargajiya A Yau
Matsayin sana’o’in gargajiya na Hausawa a yau na cikin wani hali na kaka-na-ka-yi don kuwa ba kamar a jiya ba da kowa da kowa ya dogara a kansu, a yanzu ire-iren wadannan sana’o’i sun zama bakin kyama ga matasan wannan zamani. Wannan kuwa ya faru ne saboda matasa sun fi son yin ayyuka a ma’aikatu da hukumomi da kamfanonin da Turawa suka kawo kasar Hausa wadanda za a iya samun kudi cikin dan kankanin lokaci ba kamar a ire-iren sana’o’in gargajiya na Hausawa wadanda abin da ake samu bai taka kara ya karya ba, sai dai yana biyan bukatun yau da kullum na masu yin wadannan sana’o’i.
Idan muka dauki sana’o’in gargajiya na Hausawa a yau za a fahimci cewa sun shiga wani hali na tabarbarewa wanda ya faru saboda matasan wannan zamani ba su koyi yin su ba. Misali, sana’ar noma wadda kowane mutum a kasar Hausa a jiya ya dogara a kanta domin samun abin da za a ci da kuma sayarwa, a yau matasanmu na kyamar yin wannan sana’a wanda wannan dalilin ne ya haifar da karancin abinci a wannan zamani.
Wannan kuwa, ya faru ne saboda yawan masu cin abinci ya nunka yawan masu yin sana’ar noma a yau. Wannan ba karamar matsala ce ga Hausawa ba don kuwa har yanzu ci gaban kasar Hausa bai kai matakin yin noma daidai da matakin ci gaban duniya. Akasarin manoman an dogara ne da abincin da aka noma ta hanyar noma irin na gargajiya.
A kasar Hausa a jiya ta fuskar kiwon lafiya masu gudanar da sana’o’in gargajiya sun taka muhimmiyar rawa wajen bayar da magungunan gargajiya iri daban-daban na cuttuttuka daban-daban, don kuwa wanzamai da madora da makera da mahauta da sauransu sun taimaka matuka gaya wajen bayar da magungunan cututtuka iri daban-daban. A yau, saboda matasan wannan zamani ba sun mayar da hankali wajen yin wadannan sana’o’i ba, mahaifansu wadanda suka nakalci wadannan magungunan ba su sanar da su ba. Wannan dalilin ne ya sa a yau ire-iren wadannan sana’o’i da magungunan suka bace. Saboda wadanda suka san su sun mutu ba tare da sanar da wani ba. A yau idan wata cuta ta kama mutum wadda a da can masu sana’o’in gargajiya na iya warkar da ita, sai a ce a tafi Amurka ko Turai ko Misra domin neman magani. Misali, a da can duk irin yadda kashin mutum ya karye madoran kasar Hausa na iya dora shi, amma a yau saboda matasanmu ba su mayar da hankali suka koyi yadda ake yin wannan sana’a ba, idan an yi karaya kome kankantarta, sai a ce a tafi asibitin kashi ko kuma a kai wannan mutum kasar Misra. Wannan hali na ko in kula da matasan kasar Hausa suka dauka ba karamin koma baya ya kawo wa kasar Hausa ba a wannan zamani.
Hakazalika, in ka dauki makera suma baya ga sana’arsu ta kira sukan bayar da maganin kuna, ta bangaren gudunmawar da suke bayarwa.

conned from Leadership Hausa