RASHIN INGANTA TSARO, DOKOKI DA MUKE FUSKANTA A AREWACIN NIGERIA.

Abubuwan da ke faruwa a kasar mu laifin suwaye:
1.Shuwagabannin kasar ne?
2.Al'ummar kasar ne?
3.Jami'an kasar ne?
4.Lauyoyin kasar ne?

Idan muna so kasar mu ta inganta da matakan tsaro to dole mu bi dokokin da suke a rubuce na kasar. Domin kuwa, ta haka ne kawai zamu samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a qasar mu. Muyi amfani da hankular mu, lura da irin mu'amalolin da wasun mu sukeyi.

1.Shuwagabannin qasar mu:
            Kamar yadda muka sani dole ne gomnatin kasar mu (Nigeria) ta kara matakan tsaro da dokokin hukunta duk wani mai aikata laifi komin kankantar laifin. Sannan suyi kokarin samar wa matasan mu aikin yi, su kuma samar da kayan aiki sosai kuma masu inganci, wanda zai taimake wajen cigaban kasar da zaman lafiya.Gomnatin kasar mu su sani cewa alhakin ko wane rai na kasar na wuyar su, saboda sune Shuwagabanni. Mu Al'ummar kasar(Nigeria) mun zabe ku ne domin kuyi mana aiki, ba dan kuyi suna, mulki da kudi ba, sai dan ku kawo mana sauyi da cigaba. 

2. Al'ummar kasar mu:
             Muyi amfani da hankular mu wajen sanin meye ya dace da rayuwar mu, domin muna bada gudunmawa a ta'addancin da muyagun ayyukan da akeyi a kasar mu (Nigeria). Muyi ma kawunan mu adalci, mu kuma taimaki gomnatin mu wajen inganta zaman lafiya. Idan har sai gomnati ne kawai zata yi aiki toh mun so kan mu. Mu na ganin Abu na faruwa amma baza mu yi namu kokarin ba sai muce aikin gomnati dan haka baza muyi komi ba, to lallai muna kashe kan mu ne ta hakan ma. Mu sa ido sosai wajen lura da shiga da ficen mutanen da ke kewaye da mu. Ta haka ma zamu iya taimake wa kasar mu ta gano masu aikata laifin.
 

3. Jami'an kasar mu:
             Ku ne kashin bayani duk wani inganta tsaro da ya kamata ayi a kasar mu ba ma iya arewacin Nigeria ba, harda kudanci, gabashin da yammacin kasar duka. Ku inganta ayyukan ku da gaskiya da rukon amanar da kuka yi alkawari kafin zama Jami'ai. Kuyi aiki do min kasar ku, ku hukunta dukkan wani mai laifi komin matsayin sa. Saboda idan ba ku muma ba mu, haka idan ba mu kuma ba ku domin ba wanda zaku tsare har ku kare. 

4. Lauyoyin kasar mu?
            Kun san hukunci Kala-Kala, ko wane laifi da hukuncin sa, kuma ko wane hukunci da yanayin shi. Idan har zaku iya barin mai laifi a kasar ku ba tare da hukunta shi daidai da laifukan sa ba, hakan daidai ya ke da kun ba da gudunmawar cigaba da muyagun ayyuka a kasar (Nigeria). Dan haka duk wanda aka ka mashi da laifi ko wane irin laifi ne, to doka ta ba da damar hukunta shi bisa kokarin lalata kasar sa. Kar ku zama masu kare karya ku bar gaskiya. 

 Abubuwan da muke fuskan ta:
Ana kashe mutane kamar basu da daraja, kisan yara kanana kamar basu da galihu.

Ana ma mata fyade kamar basu da kima, tozarci ga 'yan mata sai kace wulakantattu.

Ana garkuwa da mutane tamkar wasu dabbobi, an dauki rai ba'a bakin komai ba.

Ana hana matasan mu aikin yi, hakan babban matsala ne da ke janyo ta'addanci. Shi kuma ta'addanci yakan fara saboda talauci, shi kuma talauci so tari Rashin aiki ke haifar da hakan.

Kira:
Dan haka kira na ga dukkan wanda ke iya bada taimako a kan kawo karshen ta'addanci da karda muyi kasa a gwiwa, mu cigaba da daga muryoyin mu sama har sai munga karshen faruwar hakan.

Ku cigaba da bibiyan shafuka mu na sada zumunta a;
INSTAGRAM @queennerner
                        @zeekhamys
TWITTER @queennerner
                   @ZaynerbMk