Mukan iya samun hanyoyi daban daban akan yadda karatun yara mata zai kasan ce.
Na farko, zaku ga idan yanxu aka sa 'ya mace a makarantar karantar ilimin kimiyya na likitanci amfanin al'ummah ne baki daya, domin akwai fannoni da yawa da sukan dauke wa mutane, Wanda dama mace ta dace da gurbin wajen.
Ga kadan daga cikin su:
1) Haihuwa(labour)
2) Aiki(theater)
3) Duba(Scan)
1.Haihuwa (labour): Mace ce ta dace ta anshi haihuwar 'yar uwar ta mace ba tare da wani namiji ya ga jikin ta ba amma mukan samu qarancin hakan,mafi yawan mata sukan dakatar da ilimin likitanci ne a matakin diploma, Wanda hakan na qara samar Mana da qarancin manyan Likitoci qasar mu yanxu.
2.Aiki (Theater): Haka zalika wajen gudanar da aiki(theater) muna da qarancin matan da suka iya aiki a qasar mu, domin haka yasa namiji ne zewa mace aiki koda kuwa wane irin aiki ne a jikin ta, mu sani cewa wasu abubuwan basu gagare mu ba amma mukan dauka kamar sunfi qarfin mu musamman mu mata.
3.Duba(Scan): Idan muka qara la'akari Kuma da Duba(Scan) zamu ga cewa shima fa wani sashe ne da ya kamata a ce mata suna yawa a fannin, domin komin qanqancin waje a jikin mace da zai sa namiji ya gani wanda ba muharramin ta ba kuskure ne.
Dan haka akwai makarantu da dama a qasar mu Wanda zamu iya Karatun likitanci(health) zuwa matakai daban daban a duniya.
Kira ga:
Gomnati (government)
Iyaye (Parents)
Malamai (teachers)
Na farko, Kira ga malamai(teachers) akwai bukatar malamai su taka na su rawar da kuma qoqari wajen nuna muhimmancin ilimin likitanci ga 'ya mace ga al'ummah ma baki daya.
Na biyu, Iyaye(parents) har ila yau bazamu daina kai kukan mu ga Iyaye ba akan su daina hana yaran su Karatun zamani musamman a irin wannan yanayin zamanin na mu, akan kai babban mataki na likitanci a Rayuwa .
Na uku, Gomnati (government) Kira na ga gomnati a nan shi ne akwai yaran da basu da qarfi ko wata lalura da ta hana su Neman ilimin zamani, Dan Haka nake roqon gomnati da su taimaka wa yaran da basu da qarfin kai kansu makaranta domin samun ilimi ingatacce na zamani, yin hakan zai taimaki qasar mu da al'ummar qasar.
Da Haka Nake Kira Ga Yara Mata Harda Ma Manya(masu aure) Da Mu Sani Cewa Duk Karatun Da Mace Tayi Ko Zatayi baya Zama Banza Ko Wanne Da Gurbin Sa A Rayuwa
Domin qarin bayani ku bibiye mu a shafukan mu na sada zumunta
0 Comments