Haqqiqa ya kamata mu ringa suturta jikkunan mu da suturu Wanda suka dace ma'ana, wanda suka rufe Mana Duk wasu waurare da basu dace a ce Wanda ba muharramin mu su gani ba.
Alal misali yanxu zaku ga mace ta yi shiga ta fita waje ko wani guri cikin bainar jama'a maza da Mata a gurin, Amma idan ku ka ga shigar dake jikin ta ke/kai ke jin kunya ba ita da kayan ke jikin ta ba, domin ita kuwa bata damu ba.
Muna da shiga(dresses) kala daban daban a duniya, wanda wasu daga cikin suturun da Yara Mata ke sakawa Al'adun mu koh Addinin mu basu chanchanci kalan shigar ba.
Yarinya takan samu tarbiyya ne daga wajaje uku(3) zuwa hudu(4):
1. Gidan su (Home)
2. Makarantan su (School)
3. Unguwan su (Community)
Na farko Gidan su: Yarinya tarbiyyan su na farawa ne tun daga gidan su kafin ya ta wuce mataki na gaba. Wasu sutura ko shigar da Yara Mata su ke sawa tun daga qurucciyar su daga gidan su a ke koya masu, saboda duk shigar da Yarinya ta girma ta ga ana mata to tabbas mafi yawanci haka zata cigaba har girman ta.
Na biyu Makarantan su: Yara Mata sukan koyo dabi'un shigar Banza daga qawaye koh wasu daban a makaranta. Yau idan yarinya ta shirya ta fita daga gidan su, shigar da ta fito gida daban da ita, shigar da kuma zatayi a wajen gida (makaranta) shima daban. Yanxu yara mata har siyan wasu kayan su keyi su ba da ajiya a waje, saboda suna fitowa gida zasu chanza suturan dake jikin su.
Na Uku Unguwan su: Yanayin muhalli ko unguwa shima na sa Yara Mata su lalace da shigar Banza. Wanda idan mukayi la'akari da mutanen unguwan, shin na kirki ne ko na banza. Misali, wasu unguwan za mu ga akwai Gidan karuwai, Gidan giya......Bai dace mu zauna ba saboda duk shigar da suka fito dashi su Kuma Yaran na gani to lallai a kwana a tashi wata rana yaran zasu fara kalan shigar.
Yanzu zamani ya chanza suturu daban daban na banza mutanen Banza qara fito dashi sukeyi, Su Kuma Yara Mata duk wasu kayan qele qele suka fi so dan gayu.
Dan Haka da zarar kina mace kin fito da kaya masu daukan hankali kinyi ado, to ki sani cewa mala'ikun Allah tsine miki sukeyi.
Dan haka mu kiyaye shigar da muka San cewa Allah zai iya fushi da mu sannan Kuma ya kai mu ga shiga wuta (wa'iya zu billah).
0 Comments