"Zamani ya canza, dan haka dole ne a ba mata damammaki na cigaba....
Musamman a wannan zamani da muke, wanda akwai abubuwa dayawa na cigaba da a ke dashi, cigaban rayuwa, ilimin addini, ilimin zamani, da al'adu......
Har yanzu a kasar mu Nigeria wasu na daukar rayuwar mata bai da muhimmancin da ya wuce tayi aure ta zauna da yara a gidan ta. Wanda hakan, na sa wasu matan kasa a gwiwa wajen cimma burin su a rayuwa.
Mata na iya zama abin alfahari kuma a yaba a lokuta da dama. Idan har za mu ce maza ne kawai zasu zauna ko su kasance a manyan mukamai, to tabbas kasar mu ba za a cibaga ba. Mu bama mata damar kasancewa a wajaje ta yadda su ma za su bada tasu gudunmawar da shawarwari a kan cigabar kasar mu.
"Kuma babbar abunda zamuyi fada dashi shi ne rashin ilimin matan, ba suyi karatun ba ballantana su zama abin alfahari ko abin kwatance.
"Kuma Mata, ya kamata kuyi kokari da tunanin yadda za mu ga kuma ba'a bar ku a baya ba wajen samun matsayi daban-daban. Ka da ku yarda a yi watsi ko a wuce ku a abubuwa na cigaban kasar mu, domin ku ma 'yan kasa ne kamar mazan.
0 Comments