Bincike ya nuna cewa, akwai matsaloli a kasar mu wanda talla na daya daga cikin faruwan su...
Kamar su: Karancin ilimi ga 'ya'ya mata, yin ma 'ya'ya mata Fyede, mata marasa kamun kai da sauransu...

Idan muka dauki, fannin karancin ilimin yara mata za mu ga cewa, matan da su ke zuwa talla, ba dukkan su bane su ke karatu (ma'ana boko ko islamiyya) ba saboda sun fifita wannan tallar a kan ilimi.

Sannan kuma, rashin karatun yara matan na illatar da kasar mu. Domin kuwa akwai wajejen( Siyasa, tiyatar 'ya mace, koyar wa su abubuwan) da mata ne su ka dace a gurin ba maza ba. Rashin kula da wadannan abubuwan a kasar mu ya sa sauran wasu kasashen waje sukayi mana pintinkau. 

Bincike ya nuna cewa, wa su daga cikin matan da ba su da kamun kai a nan arewacin Nigeria, ya samo asali ne daga pita yawan talla. Idan Iyaye suka daura masu tallar sai su tapi yawan gantali a duniya, har sai lokacin komawan su gida yayi sai su dawo, ba da sanin Iyayen ba.

Musamman Iyaye maza, wasunsu basu san yaran na tallan ba, domin dayawan iyaye mata suke daura wa yaran talla har ya kai ga lalacewar tarbiyyar su. 

Bincike ya nuna cewa, mafiyawan 'ya'ya mata da a ka lalata masu rayuwa ta hanyar (Fyede) a arewacin kasar mu, ya na faruwa ne ta hanyar tura yara mata tallace-tallace a titi, wanda hakan ke baiwa wa su mazajen damar yin wa yaran fyede.

Ayayin da wasu mazan ke amfani da damar su na kiran yarinya lunguna, ko wasu wajajen da za su yi ma yaran fyede ba tare da angansu ba.

Dan haka, idan har kin/kasan kana daya daga cikin wanda ke tura yara talla a titi, su na bi lunguna domin siyar da abunda a ka daura musu to mu yi kokarin daina wa.

Domin hakan na daga cikin abubuwan da su ke gurbata mana kasar mu.