Idan mukayi dubiya da wannan lokaci da yanayin da qasar mu take ciki zamu ga cewa aikin gwamnati ba abin dogaro bane musamman yanzu da aiki yake wahalar samu.
Bincika ya nuna cewa, a na wahalar samun aikin gwamnati a qasar mu, saboda wasu dalilai.....

Aikin gwamnati bai tsaya kan wahalar samu ba, idan aka samu aikin ma to ba tabbas din samun ingantacce albashi mai tsoka da za'a iya biyan bukatu da su.

Haka zalika, idan aka samu aikin ma, ko da ba albashi mai tsoka, to a hakan ma sai a shafe watanni ba'a biya albashin ba. A bar ma'aikacin da buga bugan yadda zai samu kudi.

Bayan haka ma, aikin gwamnati aiki ne da a kowane lokaci za'a iya sauke mutum, ko a canza ma mutun wajen aiki, zuwa wajen da mutum bazai iya zama ba. Daga karshe sai ya zamana mutun ya rasa aikin saboda rashin samun kwanciyar hankali a wajen aikin.

Aikin gwamnati ba aikin da mutun zai saki jiki da shi bane, muyi kokarin samun wasu hanyoyin neman, domin mu iya biyan bukatun mu na yau da kullin.