Kamar yadda aka sani ne sana'ar hannu sana'a ce mai matukar amfani da dadi, musamman a irin wannan lokaci da aikin gwamnati ke wahalar samu...

Idan mukayi la'akari da irin sana'o'in da akeyi yanzu zamuga cewa da yawan mutane da sana'o'in suke iya samun abun da zasu rufawa kan su asiri.

Sana'ar hannu na da amfani ko da mutum na aikin gwamnati. Domin akwai uzurorin da za su taso wanda albashin da ma'aikacin gwamnatin ke samu ba zai iya biya masa bukatun sa duka ba.

Idan mutum na sana'ar hannu ya kanyi wahala a ce ba kudi a hannun sa ko kuma abunda zai iya sayarwa a lokacin da ya ke bukatar kudi domin biyan bukatar sa.

Kar mu raina sana'a komin kankancin ribar ta, saboda raina ribar zai iya sa sana'ar taki cigaba balle mu samu albarka a sana'ar.

Ita sana'ar hannu ba sana'ar mata bane, har maza na iya yin sana'ar hannu, domin sana'ar hannu daban-daban ne....
"Akwai sana'ar da namiji ne zai fi iyawa "Akwai sana'ar da macece zata fi iyawa

Sannan kuma, Sana'ar hannu ba ta manya ba ce kawai, hatta yara zasu iya yin sana'o'i daban-daban musamman a irin lokacin nan da ake....
Domin koya masu sana'a tun suna yara zai taimake su a gaba ta hanyoyi daban-daban... Musamman a wannan zamani da aikin gwamnati ke wahalar samu ko da kayi karatu mai zurfi.

Mu koyi Sana'o'in hannu domin gujewa dogaro da dukiyar wani...