Marayu mata su na daya daga cikin manyan abunda ya kamata mu tausaya ma a yanzu, duba da gannin yadda abubuwa ke kasance wa yanzu a duniya ba iya kasar mu ba.

Ya zamana cewa, akwai abubuwa dayawa da ba sa samu saboda rashin kulawa irin na gomnatin qasar mu. Musamman a wannan lokaci da masu Iyayen ma suna neman yadda zasu rufawa kansu asiri balle har a kula da marayun.

Idan mukayi la'akari da wasu kasashen duniya da suka cigaba, za muga cewa, ana daraja marayu musamman mata da aka sani da rauni wajen wasu abubuwan.

Marayu mata sunfi marayu maza bukatar taimakon mu, domin marayu mata sunfi fadawa cikin mugun hali ko yanayi mara kyau wajen neman yadda zasu rufawa kansu asiri.

Bincika ya nuna cewa, kimanin marayu mata da suke cikin wahalar rayuwa yanzu basa iya kirguwa saboda rashin taimakon su da ba'ayi.
Wasu marayun mata sun fada harkar karuwanci, lesbian, shaye-shaye, har ta'addanci (kisa) saboda neman abun duniya.

Haka zalika, marayu mata yanzu da basa zuwa makaranta manya da yara sunfi miliyan (1,000 000) kuma hakan ya samo asali ne Saboda rashin so da ake nuna masu. 

Idan har zamu nuna masu soyayya ta hanyar jawo su a jikin mu to tabbas za'a rage marayu mata da suke lalacewa a kasar mu.

Wasu mutanen su kanyi tunanin cewa, marayu mata ba su da sauran gata ko mutuncin da za'a iya san su, ya zamana cewa ana wulakanta su da kuma mai da su kamar bayi.
Sannan mafi muni da takaicin abin shi ne 'yan Uwan wadannan marayun su suka fi wulakanta su tamkar ba jinin su ba.

Kasan cewar Iyayen yarinya sun rasu, hakan ba zai bamu damar wulakanta su ko mu cutar da su ba, domin su ma mutane ne kamar mu.

Dan haka, ya kamata mu sani cewa idan muka taimake su tamkar mun taimaki yaran mu ne, haka idan muka wulakanta su ko muka cutar da su kamar yaran mu muka cutar.