Karatun lauya, karatu ne da mata za su iya yi musamman yanzu da ake cin zarafin mata sosai ake wulakanta su.

A zamanin da babu mata lauyoyi sosai maza sunfi karantar course din, saboda ana tunanin karatun ya fi dacewa da namiji ba mace ba. Hakan yasa ba'a barin mata suna yi. Idan muka qara komawa baya za muga cewa, idan wani abu ya faru da mace a zamanin da, ba'a daukan mataki saboda ganin ita mace ce. 

Zamani ya canza yanzu, Saboda cases da dama na mata za muga lauyoyi mata keyin case din, ba dan komai ba sai dan su kwatar masu cikakken 'yancin su.

Cases na mata yanzu na matsalolin gida (family issue) za muga lauyoyi mata suke wucewa gaba akan shari'ar, ba dan komai ba sai dan akwai maganganun da ita macen ba zata iya fadiwa lauya namiji ba saboda kunya da sauransu.....

Haka zalika, cases na fyade (rape) da mata ke fuskanta yanzu sosai, lauyoyi mata su ne za su iya tambayar wacce fyaden ya faru da ita kuma ta fada masu komai, ta yadda za'ayi shari'a da kyau har a kwatar mata 'yancin ta.

Idan akwai lauya mace matsaloli ko cutarwa da akai ma mutum za ta iya kawo karshen su, ta hanyar amfani da dokoki da kasar mu ta tanada domin hukunta masu irin laifin ba sai anje kotu ba.

Idan ba lauyoyi mata zai zamana, akwai mutane da yawa da ake zalunta wanda ko sun shari'ar akeyi ba komai zasu fadi ba saboda namiji ne lauyan. Akwai mutanen da sunfi san aiki na shari'a da mace lauya.

Akwai mataki na shari'ar da idan aka kai sai an nemi lauya mace ko da case din maza ne, saboda mace ce zata iya abunda ake so a wajen, to idan babu lauya mace abun bazai tafi yadda ya kamata so ba.

Dan haka, mu na matukar bukatar lauyoyi mata a cigaban kasar mu domin yaki da wasu haramtattun ayyukan da muke fuskantar a yanzu.