Cikin matsalolin da muke fuskanta a yanxu ta fannin Cigaban ilimin 'ya mace, ko na matar aure ko na budurwa musamman ma a yanxu da abubuwan qasar mu suke lalacewa ta fannin karatun zamani.
Dole a cikin matsalar cigaban karatun 'ya mace baza'a rasa daya daga cikin wadannan abubuwa din ba da zan lissafo...
Talauci
Iyaye
Aure
Al'adu
 Talauci na iya dakatar da karatun 'ya mace ta ko wane irin hanya da kuma yanani na rayuwa, dan haka idan har zamu cigaba da haka to tabbas ilimin mata bazai yiwu mana ba, akwai kungiyoyi masu zaman kansu dama na gomnati wa'yanda zasu iya tallafa ma marasa qarfi akan cigaban karatun mace, kuma akwai sana'o'i wanda zamu iyayi na gida wanda idan muka riqe su zamu iya biyan ma kanmu kudin karatun mu da kan mu ba tare da wani ma ya taimake mu ba.

Iyaye suna bada nasu gudunmawan akan rashin ilimin 'ya'ya mata a yanxu, domin kuwa da zarar sunga yarinya ta girma to fa zasu daina mata kallon 'yar makaranta saidai matar aure kuma a zaman gida to gaskiya iyaye suma ya kamata suyi mana tinani akan ilimin yara mata, kasashen da suka cigaba basa wasa da ilimin 'ya mace don haka ne ma idan kaga da namiji a wani matsayi ko wani mukami to tabbas zaka ga wata mace da take da irin wannan matakin akai, dan haka ina kira ga iyaye mata da suyi tunani akan ilimin yaran su mata.

Aure wannan shine babban abinda ke dakatar da karatun mata tun asali bama a yanxu aka bullo dashi ba, mata marasa zurfin tunani sukan dauka cewa dawainiya da hidindimu na aure na hana cigaban ilimin su, musamman ma idan suka fara haihuwa.Tabbas ansan cewa hidimar kulawa da iyali ba abu bane qarami, amma idan muka yi nazari da kuma tsara al'amuran mu cikin tsari zamu iya yin karatu a gidajen mu na aure, mu sani cewa fa idan muka yadda karatun mu yana tsayawa saboda aure to lallai za'a bar mata a baya a kasar mu domin zasu zama tamkar basa rayuwa a kasar, zai zamana cewa muma bamu bawa kasar mu gudunmawa ba, mu samu ingantaccen ilimi shine ma zaisa mu baiwa yaran mu tarbiyya mai kyau da kuma sannin yadda zamu gudanar da tsarin rayuwar mu cikin hikima da hankali.

Al'adu muna da al'adu daban daban wadan da har yanzu suke janyo cikas akan ilimin 'ya'ya mata, kuma wanda wannan al'adun basu da wani kwakkwaran dalili na hana mata cigaba da karatu, dan haka yanzu zamani yazo da dole zamu aje wadannan al'adun domin amfanan qasar mu baki daya, ilimin 'ya mace baida zababbun al'adu da za'a ce sune zasuyi karatu, sannan babu wasu shekaru da za'ace mace ta daina neman ilimin domin kuwa shi karatu baya tsufa haka kuma ba'a tsufa akan neman sa.

Dan haka ya kamata mu baiwa 'ya'ya mata ingantaccen ilimin daya dace su sama.