Yara kanana da basu wuce shekara 6 zuwa 12 ba suna almajiranci. 'Yan mata budurwaye su na almajiranci yanzu a kasar mu. Har ta Iyaye mata wadanda ke almajirancin sun dauki almajiranci kamar sana'ar yi.
Idan mukayi la'akari da kananan yara matan da ke yawo a titi da sunan almajiranci za mu ga cewa, laifin ba daga yaran bane na Iyayen su ne. Domin kuwa yarinyar ba ta da laifi, saboda idan har Iyayen sun ba ta kulawa kuma su na kokarin sauke haqqin su akan yarinya to ba yadda za ta fita waje almajiranci a matsayin ta na yarinya karama.
"Cikin yara matan da ake dauka a na siyarwa, rabin su almajirai ne...
Bincike ya nuna cewa, 'yan mata budurwaye da su ke almajiranci yanzu sunyi yawa, za ku ga budurwa ta pito almajiranci saboda ta biya wa kanta wasu bukatun ta na yau da kullin. Wasu daga cikin yara matan, Iyaye basu da karfin siya masu wasu abubuwan, wanda hakan ke sa su pita domin neman taimako.
Yawon bara da su ke pita na sa su shiga cikin wani mugun hali, wanda wasu daga nan su ke haduwa da mutanen banza har su lalace,su fara shaye-shaye, karuwanci da sauran su...
Mutuwar zuciya ya sa wasu iyaye mata lalata rayuwar su saboda almajiranci da suka dauka sana'ar yi. Idan har Iyaye mata ba za su yi sana'a komin kankantar riba ba, domin kiyaye mutunci da kimar masu na mata ba, to ba yadda yara mata kanana ko budurwaye su dai na pita yawon almajiranci a titi.
Cikin hiran da mukayi da wasu daga cikin iyaye mabaratan sun bada dalilen cewa, talauci ya sa su ke pita almajirancin, cikin su akwai ma su yara, wa su ma da auren su. Babu wani dalili mai karfi, domin kuwa akwai kungiyoyi na gomnati da kuma kungiyoyi masu zaman Kansu da a ke da su na taimakon marasa karfi domin yanzu a kasar mu.
"Kiran mu ga gomnatin kasar mu, a kan su kara karfi wajen yakar almajiranci a kasar nan domin rage faruwar wasu matsalolin mu.
1 Comments
Allah ya sa mu dace
ReplyDelete