Binciken da masana sukayi ya nuna cewa, talla a wajen 'yan mata ya zama ruwan dare, sakamakon matsanancin talauci da kuma kokarin rufawa kai asiri.
An kuma lura cewa, jihohin arewacin kasar nan, sun fi kowanne samun 'yan talla musamman 'yan mata, wadanda ke fuskantar kalubale daban-daban daga masu siyar kayayyakin na su.
An lura cewa, Iyaye mata ke dorawa yara talla musamman 'yan mata, ba tare da yin la'akari da lokutan zuwa makaranta ba, wanda hakan na baiwa yaran kwarin gwiwar kin zuwa makaranta, sakamakon sabo dayin tallar.
Sannan wasu Iyayen kan nuna cewa, da talla yarinya za ta tara abun da za a kai ta daki da shi, saboda ganin cewa ba su da karfin siyawa yaran idan lokacin ya zo.
Idan har wannan shi ne talla, kuma hakan su ne dalilin sa yaran su musamman mata zuwa talla, ya kamata mu yaki hakan a kasar mu, ta banyan taimakon Iyayen su, domin su dai na tura yaran su talla.
1 Comments
Bravo alaik
ReplyDelete